QuranQuiz bySALSABIL STUDIO
Open the appOpen app

سورة التكوير

Suratul At-Takwir da Hausa

Ayoyi 29 · Sura ta 81 cikin 114

🌐 Translation: Hausa

Englishالعربية (بلا ترجمة)اردوBahasa IndonesiaBahasa MelayuTürkçeFrançaisDeutschEspañolPortuguêsItalianoNederlandsРусскийفارسیবাংলাहिन्दीSoomaaliKiswahiliHausaShqipBosanskiAzərbaycancaOʻzbekcha中文日本語한국어ภาษาไทยTiếng ViệtTagalogپښتوPolskiSvenskaNorskSuomiČeštinaRomânăБългарскиУкраїнськаעבריתதமிழ்മലയാളംతెలుగుमराठीગુજરાતીनेपालीසිංහලঅসমীয়াسنڌيدریKurdîދިވެހިئۇيغۇرچەአማርኛAfaan OromooYorùbáKinyarwandaBamanankanChiyaoTamaziɣtMëranawТоҷикӣҚазақшаТатарчаភាសាខ្មែរEnglish (Abdel Haleem)

Fassara: Abubakar Gumi

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

إِذَا ٱلشَّمْسُ كُوِّرَتْ ﴿١﴾

81:1 Idan rãna aka shafe haskenta

وَإِذَا ٱلنُّجُومُ ٱنكَدَرَتْ ﴿٢﴾

81:2 Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani).

وَإِذَا ٱلْجِبَالُ سُيِّرَتْ ﴿٣﴾

81:3 Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su.

وَإِذَا ٱلْعِشَارُ عُطِّلَتْ ﴿٤﴾

81:4 Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba.

وَإِذَا ٱلْوُحُوشُ حُشِرَتْ ﴿٥﴾

81:5 Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su.

وَإِذَا ٱلْبِحَارُ سُجِّرَتْ ﴿٦﴾

81:6 Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta.

وَإِذَا ٱلنُّفُوسُ زُوِّجَتْ ﴿٧﴾

81:7 Kuma idan rãyuka aka haɗa su da jikunkunansu.

وَإِذَا ٱلْمَوْءُۥدَةُ سُئِلَتْ ﴿٨﴾

81:8 Kuma idan wadda aka turbuɗe ta da rai aka tambaye ta.

بِأَىِّ ذَنۢبٍ قُتِلَتْ ﴿٩﴾

81:9 "Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?"

وَإِذَا ٱلصُّحُفُ نُشِرَتْ ﴿١٠﴾

81:10 Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su).

وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ كُشِطَتْ ﴿١١﴾

81:11 Kuma idan sama aka fẽɗe ta.

وَإِذَا ٱلْجَحِيمُ سُعِّرَتْ ﴿١٢﴾

81:12 Kuma idan Jahĩm aka hũra ta

وَإِذَا ٱلْجَنَّةُ أُزْلِفَتْ ﴿١٣﴾

81:13 Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita.

عَلِمَتْ نَفْسٌ مَّآ أَحْضَرَتْ ﴿١٤﴾

81:14 Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan).

فَلَآ أُقْسِمُ بِٱلْخُنَّسِ ﴿١٥﴾

81:15 To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã ba.

ٱلْجَوَارِ ٱلْكُنَّسِ ﴿١٦﴾

81:16 Mãsu gudu suna ɓũya.

وَٱلَّيْلِ إِذَا عَسْعَسَ ﴿١٧﴾

81:17 Da dare idan ya bãyar da bãya.

وَٱلصُّبْحِ إِذَا تَنَفَّسَ ﴿١٨﴾

81:18 Da sãfiya idan ta yi lumfashi.

إِنَّهُۥ لَقَوْلُ رَسُولٍ كَرِيمٍ ﴿١٩﴾

81:19 Lalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah.

ذِى قُوَّةٍ عِندَ ذِى ٱلْعَرْشِ مَكِينٍ ﴿٢٠﴾

81:20 Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi.

مُّطَاعٍ ثَمَّ أَمِينٍ ﴿٢١﴾

81:21 Wanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce.

وَمَا صَاحِبُكُم بِمَجْنُونٍ ﴿٢٢﴾

81:22 Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne.

وَلَقَدْ رَءَاهُ بِٱلْأُفُقِ ٱلْمُبِينِ ﴿٢٣﴾

81:23 Kuma lalle ne, yã gan shi a cikin sararin sama mabayyani.

وَمَا هُوَ عَلَى ٱلْغَيْبِ بِضَنِينٍ ﴿٢٤﴾

81:24 Kuma shi, ga gaibi bã mai rowa ba ne.

وَمَا هُوَ بِقَوْلِ شَيْطَـٰنٍ رَّجِيمٍ ﴿٢٥﴾

81:25 Kuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce.

فَأَيْنَ تَذْهَبُونَ ﴿٢٦﴾

81:26 Shin, a inã zã ku tafi?

إِنْ هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ لِّلْعَـٰلَمِينَ ﴿٢٧﴾

81:27 Lalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai.

لِمَن شَآءَ مِنكُمْ أَن يَسْتَقِيمَ ﴿٢٨﴾

81:28 Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu.

وَمَا تَشَآءُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلْعَـٰلَمِينَ ﴿٢٩﴾

81:29 Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda.

Gwada kanka

Gwada kanka →

Hear Surah At-Takwir from all 90 reciters →